Murna-ta-koma-ciki: Gwamnatin tarayya ta kifewa ma'aikata ciki game da karin albashi

Murna-ta-koma-ciki: Gwamnatin tarayya ta kifewa ma'aikata ciki game da karin albashi

Babban ministan harkokin kwadago da ma'aikata a gwamnatin shugaba Buhari Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa da wuya ne fa sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta ayyana tana son fara baiwa ma'aikata ya fara aiki a watan Satumba mai zuwa.

Kamar dai yadda ministan ya bayyana, a watan Satumba mai zuwa ne dai kwamitin da gwamnatin ta kafa domin lalubo fitacciyar hanya da za'a dabbaka karin albashin zai kammala aikin sa.

Murna-ta-koma-ciki: Gwamnatin tarayya ta kifewa ma'aikata ciki game da karin albashi

Murna-ta-koma-ciki: Gwamnatin tarayya ta kifewa ma'aikata ciki game da karin albashi

KU KARANTA: Maguzawa 90 sun musulunta a Kano

Legit.ng ta samu cewa sai dai Mista Ngige har ila yau ya bayyana cewa daga wannan lokacin ne ita kuma gwamnatin tarayya za ta soma yin nazari game da rahoton tare da neman hanyar da zata tabbatar da shi.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan siyasar na dake zaman tsohon dan majalisar wakilai da kuma majalisar dattijai kuma dan asalin jihar Kaduna, Sanata Baba-Ahmad ya yi kaca-kaca da kurarin da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na cewa tana yakar cin hanci da rashawa.

Sanatan a yayin wata fira da yayi da wakilin majiyar mu ta Daily Trust ya bayyana cewa yaki da cin hanci da rashawar da shugaban kasar ke wakar yana yi tamkar bita-da-kulli ne kawai domin cin zarafin wasu adawa da shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel