Zaman da muka yi a Gidan Kaso ya daga daraja mu a nahiyyar Afirka - Orbih

Zaman da muka yi a Gidan Kaso ya daga daraja mu a nahiyyar Afirka - Orbih

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Edo, Cif Dan Orbih, ya bayyana cewa kwana gudan da suka shafe da sauran jiga-jigan jam'iyyar na jihar a gidan kaso na birnin Benin ta daga darajar su da a halin yanzu sun zamto dattawa a nahiyyar Afirka.

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne kotu da sanadin hukumar EFCC ta garkame Cif Orbih da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP na jihar Edo a gidan kaso bisa zargin su da aikata laifin almundahanar dukiyar gwamnati.

Sauran wadanda suka shafe daren ranar Juma'ar da ta gabata a gidan kaso sun hadar da; Fasto Osagie Ize-Iyamu, Mista Lucky Imausuen, Tony Azegbemi da kuma Efe Anthony bayan sun gaza ciki sharuddan beli da Alkali P.I Adojokwu ya gindaya.

Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin jiga-jigan jam'iyyar da aikata laifin almundahana ta kimanin Naira Miliyan 700 tun a shekarar 2015 da ta gabata.

Zaman da muka yi a Gidan Kaso ya daga daraja mu a nahiyyar Afirka - Orbih

Zaman da muka yi a Gidan Kaso ya daga daraja mu a nahiyyar Afirka - Orbih

Kotun tana zargin wannan kudade wani kaso ne cikin Dalar Amurka Biliyan 115 a tsohuwar Ministan kudi, Diezani Allison Madueke ta wawushe daga asusun gwamnatin domin yakin neman zaben 2015 kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KARANTA KUMA: Ka tabbata an gabatar maka da sakamakon bincike akan magudin Kasafin Kudin 2016 - Kotu ga Shugaba Buhari

Rahotanni sun bayyana cewa, kotun ta bayar da belin su ne da misalin karfe 10.30 na yammacin ranar Juma'ar da ta gabata.

A yayin gabatar da jawabai ga magoya bayan sa da suka ziyarce shi a gidan sa, Cif Orbih ya bayyana cewa da yawan mutane sun shafe tsawon shekaru a gidan wakafi kuma suka jagoranci al'umma da rike mukamai a yayin kammala zaman su na dauri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel