Yadda sakamakon wani bincike ya gaskata furucin Buhari a kan ‘yan Najeriya

Yadda sakamakon wani bincike ya gaskata furucin Buhari a kan ‘yan Najeriya

A watannin baya da suka wuce, shugaba Buhari ya yi wani kalami da ya jawo barkewar cece-kuce tsakanin mutanen Najeriya.

Shugaba Buhari ya sha suka ne bayan ya furta cewar ‘yan Najeriya basu da hakuri. Sai ga shi wani bincike na baya-bayan nan da ya fito a yau, Talata, ranar da ‘yan Najeriya ke murnar ranar dimokradiyya, ya saka ‘yan Najeriya cikin mutane mafi yawan korafi da gwamnati.

Rahoton da wata kungiya, Good Governance, ta wallafa ya bukaci ‘yan Najeriya su canja tunanin su dangane da irin kallon da suke yiwa masu mulki da kuma yadda ita kan ta gwamnatin ke biyan bukatun jama’ar ta.

Yadda sakamakon wani bincike ya gaskata furucin Buhari a kan ‘yan Najeriya

Muhammadu Buhari

Kungiyar ta ce binciken ta ya tabbatar mata da cewar ‘yan Najeriya na daga sahun gaba a cikin ‘yan kasashen dake korafi kan gwamnati.

Ko a kwanakin baya saida kalaman shugaba Buhari na “cima zaune”, ya kara jawo barkewar wata sabuwar cece-kuce a Najeriya.

DUBA WANNAN: Muhimman abubuwa 5 da shugaba Buhari ya fada a jawabin sa na yau

Jama’ar Najeriya na yawan yin korafi da gwamnati yayin da take mulki amma da zarar an samu canji sai su fara cewa gara ma gwamnatin baya.

Ko a lokacin mulkin jam’iyyar PDP saida tsohon shugaban kasa Jonathan ya taba cewa shine shugaba da yafi shan suka a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel