Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

A ranar Litinin din da ta gabata ne mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yayi ganawar sirrance tare da mambobin sabuwar jam'iyyar PDP dake cikin karkashin lema ta jam'iyyar APC.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan ganawa ta gudana ne harabar gidan mataimakin shugaban kasar ta Aguda dake cikin fadar shugaban kasa a garin Abuja.

Mambobin sabuwar jam'iyyar sun nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana fushin da gwamnatin jam'iyyar APC ta haifar a gare su.

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Cikin Hotuna: Osinbajo yayin ganawa da tawagar jam'iyyar nPDP

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin da mataimakin shugaban kasa ya jagoranci tawagar gwamnatin APC, shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki ya jagoranci tawagar sabuwar jam'iyyar PDP.

KARANTA KUMA: Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tawagar gwamnatin APC ta hadar da; mataimakin shugaban jam'iyyar na yankin Arewa; Lawal Shu'aib, Ministan Shari'a, Abubakar Malami, mataimakin shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Ade Ipaye da kuma babban mai bayar da shawara akan harkokin tsaro na kasa, Babagana Monguno.

Tawagar sabuwar jam'iyyar PDP ta hadar da; kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa; Kawu Baraje, Gwamna Abdulfatai na jihar Kwara, tsohon gwamnan jihar Adamawa; Murtala Nyako, Barnabas Gemade, Danjuma Goje, Sanata Rabi'u Kwankwaso da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel