Ba bu lallai Mafi 'Karancin Albashi ya samu shiga zuwa watan Satumba - Ngige

Ba bu lallai Mafi 'Karancin Albashi ya samu shiga zuwa watan Satumba - Ngige

Tsammanin ma'aikatan kasar nan akan tabbatar da sabon mafi karancin albashi zuwa watan Satumba na shekarar 2018 na neman disashewa yayin da gwamnatin tarayya ta bayyana matsayar ta dangane da lamarin albashin ma'aikata.

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta bayyana cewa babu lallai mafi karancin albashin ma'aikatan ya samu shiga a kasar nan zuwa watan Satumba yayin da ta bayyana cewa, watan na Satumba shine lokacin da zata kammala tuntunbe da neman shawarwari akan lamarin.

Ministan kwadago na Najeriya, Sanata Chris Ngige, shine ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a gidan sa dake babban birnin kasar nan na Abuja.

Ministan ya bayyana cewa, ana tsammanin kwamitin sabon mafi karancin albashin ma'aikata zai kammala kididdigar sa zuwa watan Satumba kana ya gabatar da sakamakon ga gwamnatin domin shawarwari da amincewa inda za ta mika shi ga majalisar dokoki ta kasa domin neman yarda.

Ministan 'Kwadago; Chris Ngige

Ministan 'Kwadago; Chris Ngige

Sai dai ministan ya bayyana cewa, hali gami da karfin ikon biyan wannan sabon mafi karancin albashin ga ma'aikatan shine abin dubawa da nazari da gwamnatin kasar nan ke famar tuntube-tuntube da neman yarjejeniyar gwamnatocin jihohi da kuma ma'aikatu masu zaman kansu.

Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin yarjejeniyar ta takaita ne a tsakanin N22, 000 zuwa N58, 000 na albashin ma'aikata a kowane wata, inda wasu gwamnonin kasar nan ke neman a sauya tsarin kasafin jihohi da kananan hukumomi na kudaden shiga da suke samu.

KARANTA KUMA: Wani Magidanci ya yiwa 'Kanwar Matarsa 'Yar Shekara 14 Fyade a Jihar Legas

Ya kara da cewa, wasu jihohin sun nemi da a ci gaba da dabbaka yadda ake biyan ma'aikata a kasar nan sakamakon yadda wasu jihohin a halin yanzu suka gaza wajen biyan ma'aikata mafi karancin albashi na N18, 000.

A yayin haka kuma ministan ya nemi ma'aikatan lafiya dake tsaka da yajin aiki a kasar nan a kan su koma bakin aikin su yayin da ake ci gaba da tafka muhawara da tuntube-tuntuben shawarwari domin sasantawa da gwamnatin tarayya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel