Rikicin Benuwe: Yansanda sun yi caraf da wasu miyagun mutane 3 dake kera bindigu

Rikicin Benuwe: Yansanda sun yi caraf da wasu miyagun mutane 3 dake kera bindigu

Rundunar Yansandan jihar Bauchi ta bankado wata haramtacciyar kamfanin da ake kera bindigu a Oju dake cikin karamar hukumar Oju na jihar, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamishinan Yansandan jihar, Fatai Owoseni ne ya bayyana a ranar Talata 29 ga watan Mayu, inda yace sun samu nasara cafke mutanen da ke kera bindigun, da suka hada da Kingsley Abi da mahaifinsa Abi Odah, da Thomas Ode.

KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Wani dan kungiyar ta’addanci ya kashe Yansanda guda 2

Kwamishina Fatai yace Yansanda sun gano kamfanin ne a yayin da suke gudanar da bincike kan wani laifin fyade da ake zargin Kingsley da wani abokinsa da shi, a yayin da ake musu tambayoyi ne aka gano ashe Kingsley na da hannu cikin masu samar ma miyagun mutane makamai a jihar.

Kingsley da abokinsa da Babansa

Rikicin Benuwe: Yansanda sun yi caraf da wasu miyagun mutane 3 dake kera bindigu

Da aka zurfafa bincike sai Yansanda suka kai samame shagon mahaifin Kingsley, wanda makeri ne, anan ne jami’an Yansanda suka bankado muggan makamai da yake kerawa. Sai dai Mahaifin ya musanta zarge zargen dake kansa, inda yace dukkanin makaman da Yansandan suka gani ba nasa bane, yace yana hada ma mafarauta ne.

Daga karshe Kwamishina Fatai Owoseni yace zasu cigaba da gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala zasu gurfanar da mutanen gaban Kotu don su fuskanci hukunci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel