Ka tabbata an gabatar maka da sakamakon bincike akan magudin Kasafin Kudin 2016 - Kotu ga Shugaba Buhari

Ka tabbata an gabatar maka da sakamakon bincike akan magudin Kasafin Kudin 2016 - Kotu ga Shugaba Buhari

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Nation sun bayyana cewa, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jihar Legas, ta umarci shugaban kasa Muhammadu Buharu akan ya gaggauta bayar da umarnin gabatar masa da sakamakon bincike akan magudin kasafin kudin 2016.

Kotun ta umarci shugaba Buhari akan ya tabbatar da hukumomin tsaro da na masu hana yiwa tattalin arziki zagon kasa sun gabatar ta masa da sakamakon bincike akan magudi gami da satar wani kaso cikin kasafin kudin shekarar 2016 da ta gabata.

Legit.ng ta fahimci cewa, ana zargin wasu jiga-jigai na majalisar dokoki ta kasa da laifin almundahanar wani kaso na kimanin Naira Miliyan 481 cikin kasafin kudin 2016.

Ka tabbata an gabatar maka da sakamakon bincike akan magudin Kasafin Kudin 2016 - Kotu ga Shugaba Buhari

Ka tabbata an gabatar maka da sakamakon bincike akan magudin Kasafin Kudin 2016 - Kotu ga Shugaba Buhari

Mai Shari'a Muhammad Idris, shine ya bayar da wannan umarni ga shugaba Buhari akan ya umarci lauyan kolu kuma ministan shari'a na Najeriya, Abubakar Malami da kuma dukkanin hukumomi masu hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wajen gaggauta gurfanar da 'yan majalisar masu hannu cikin badakalar kasafin kudin.

KARANTA KUMA: Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki

Babban Alkalin ya gabatar da wannan umarni ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin da cibiyar kula da hakki na tattalin arziki watau SERAP (Socio-Economic Rights and Accountability Project) ta shigar da korafin ta.

Kungiyar mai zaman kanta ta SERAP da ta shahara da akidar kulawa da kuma tattalin dukiyar kasa, ta shigar da wannan korafi da sanadin wani shugabanta, Timothy Adewale, domin tabbatar da adalci akan dukiyar kasa.

Kotun ta kuma umarci shugaba Buhari akan ya tabbatar da an alkinta Naira Biliyan 131 cikin kason kudin man fetur wajen gudanar da aikace-aikacen kasa domin tsarkaka daga rashawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel