Gwamnatin tarayya za ta samar wa da matasa 500,000 aiki zuwa shekarar 2020

Gwamnatin tarayya za ta samar wa da matasa 500,000 aiki zuwa shekarar 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana shiryen-shiryen gwamnatinsa na kirkiro da ayyuka 500,000 zuwa shekarar 2020 wanda hakan zai taimaka wajen rage rashin ayyukan yi da ake fama dashi a kasar.

A cikin kwanakinan gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan wasu sassan tattalin arzikin Najeriya wanda suka hada da fanin noma da sufuri da masana'antu da kuma wutan lanatarki da iskar gas.

KU KARANTA: An bukaci Buhari ya hukunta 'yan majalisar da suka saci biliyan N481bn

A jawabinsa na ranar demokradiya da ya yi, shugaban kasa ya ce akwai alamun samar da ayyuka da kuma janyo hankalin masu saka jari a wadannan fanonin na misalin zunzurutun $22.5 biliyan kuma ana sa ran samar da ayyuka sama da 500,000 a shekarar 2020.

Albishirinku: Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka sama da 500,000 ga 'yan Najeriya

Albishirinku: Gwamnatin tarayya za ta samar da ayyuka sama da 500,000 ga 'yan Najeriya

Gwamnatin shugaba Buhari ta kirkiri shirin N-Power wanda akayi don samar wa matasa da suka kammala jami'o'in ayyukan yi.

Shugaban kasan ya ce a halin yanzu an dauki matasa 200,000 kuma akwai wasu 300,000 da aka tantance kuma nan ba da dadewa ba za'a watsa su zuwa wurare daban-daban a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.

Bayan haka, an zabi wasu dalibai 20,000 da basu kammala karatu ba don fara wata shiri na N-Build wanda gwamnati keyi da hadin gwiwar Hukumar masanan kera motoci da kuma Cibiyar magina ta Najeriya.

Shugaban kasa ya kuma ce gwamnatinsa da taka rawar gani wajen inganta rayuwar matasa da sauran al'ummar Najeriya cikin shekaru uku da suka gabata kuma za ta cigaba da kari a kan abin da ta ke yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel