Ranar demokradiyya: ‘Yan Najeriya yanzu sun bayar da rahoton cewa an rage amfani da janareta - Buhari

Ranar demokradiyya: ‘Yan Najeriya yanzu sun bayar da rahoton cewa an rage amfani da janareta - Buhari

- Mutanen Najeriya da dama suna bayar da rahoton cewa sun rage yawan amfani da inji mai bayar da wutar lantarki sakamakon Karin da aka samu na samun wutar lantarki, kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana

- Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan ne a sakonsa ga ‘yan Najeriya na bikin ranar dimokuradiyya na wannan shekarar

- A ranar Talata, shugaban kasa yayi jawabi akan cigaba da rarraba kiyasin kudin wutar lantarki ga masu amfani da ita

Mutanen Najeriya da dama suna bayar da rahoton cewa sun rage yawan amfani da inji mai bayar da wutar lantarki sakamakon Karin da aka samu na samun wutar lantarki, kamar yadda shugaba Buhari ya bayyana, a ranar Talata.

Shugaba Muhammadu Buhari, ya bayyana hakan a sakonsa ga ‘yan Najeriya na bikin ranar dimokuradiyya na wannan shekarar.

A ranar Talata, shugaban kasa yayi jawabi akan cigaba da rarraba kiyasin kudin wutar lantarki ga masu amfani da ita.

Ranar demokradiyya: ‘Yan Najeriya yanzu sun bayar da rahoton cewa an rage amfani da janareta - Buhari

Ranar demokradiyya: ‘Yan Najeriya yanzu sun bayar da rahoton cewa an rage amfani da janareta - Buhari

Lamarin na bayar da kiyashin kudin wutar lantarki ya dade yana faruwa a kasar, wanda hakan ne ya sanya gwamnatin tarayya ta matsawa kamfanin kula da harkokin wutar (DISCOs) dasu kara jajircewa don ganin sun samawa kowane mai amfani da wutar lantarki na’ura mai kididdige wutar lantarki da akayi amfani da ita.

KU KARANTA KUMA: Idan ma ka so kana iya canja mana suna – Majalisa ta maida martani ga Jega

A jawabin shugaba Buhari na ranar Dimokuradiyya, ya bayyana kudurin gwamnatinsa na barin duk wadanda keda ra’ayin a doka wurin magance matsalar kiyashin kudin wutar lantarki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel