Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama

Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama

Akalla yan mata daliban sakanadari 15 ne wasu miyagun mutane suka yi fyade a wata makarantar kwana mai suna Methodist Girls Model Secondary School dake garin Ovim Isuikwuato, jihar Abia, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani na Twitter, Kayode Ogundamisi ne ya fitar da labarin a shafinsa, inda yace lamarin ya auku ne da misalin karfe 2 na daren Juma’a, 25 ga watan Mayu, inda gungun matasan suka afka makarantar.

KU KARANTA: Bahaushe mai ban haushi: Uwargida ta maka Uban ýaýanta gaban Kotu kan watsi da yaransu

Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama

Yar majalisa da Chidinma

Da shigarsu dakunan kwanan daliban, sai suka umarcesu da kowa ya cire kayansa, tsirara haihuwar uwarsa, tare da yi musu barazanar duk wanda ya kauce ma umarninsu zasu kashe ta, suna nuna musu wasu karafa da suke dauke dasu.

Guda cikin daliban, Chidinma Nwadubem yar aji hudu ta shaida ma yar majalisa mai wakiltar mazabar Isuikwuato- Umunneochi, Nkiruka Onyejiocha a lokacin da ta kai ziyara makarantar, inda tace mutanen suna bi gado gado ne suka tashin daliban.

“Shi ne ya fada mana cewa sun kashe Maigadin makarantar, kuma sun mamaye makarantar don haka dole mu basu hadin kai, idan kuma ba haka ba zasu kashe mu, amma duk da haka wasunmu bamu yarda mun tube kayanmu ba, hakan ya sa suka fara dukanmu da rodi.

“Mun fada musu sai dai su kashe mu ba zamu tube ba, daga nan sai muka kwala ihu muna neman taimako, ganin haka ne suka farfasa mana kai da karafa, sa’annan suka tsallake Katanga.” Inji ta.

Miyagun mutane sun afka makarantar Mata, sun yi ma 15 fyade sun jikkata da dama

Daliban

Ita ma shugaban makarantar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace tuni suka mika korafi ga jami’a Yansanda don ganin sun kamo masu hannu cikin lamarin, sa’annan ta yi kira ga gwamnati da ta taimaka ta katange musu bayan makarantar.

Ita ma yar majalisar a nata jawabin, ta jajanta ma makarantar, sa’nnan tayi alkawarin yin bakin kokarinta don ganin an kamo miyagun mutanen, sa’nnan zata sake gina katangar makarantar, tare da gyaran duk winduna da Kofofin da aka fasa, haka zalika ta yi ga gwamnatin tarayya da ta karfafa tsaro a kwalejin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel