Yanzu-yanzu: Tsohon kakakin jam’iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC

Yanzu-yanzu: Tsohon kakakin jam’iyyar PDP ya sauya sheka zuwa APC

Tsohon kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, kuma dan takaran gwamnan jihar Ekiti, Prince Dayo Adeyeye, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress APC.

Tsohon kakakin jam’iyyar ya taba karamin ministan ayyuka karkashin gwamnatin PDP, amma yanzu zai hada kai da ministan ma’adinai, Kayode Fayemi domin kwato mulki daga hannun gwamnan jihar, Ayodele Fayose.

Prince Dayo Adeyeye ya fitar da jam'iyyar PDP ne sanadiyar lallasashi da mataimakin gwamnan jihar kuma dan takaran gwamnan, Olusola Eleka, yayi a zaben fidda gwamnin jam'iyyar PDP da akayi kwanakin baya.

KU KARANTA: Mahaddacin Alkur'ani ya rigamu gidan gaskiya

An fara samun jita-jitan barin jam'iyyar PDP dinsa jim da akadan bayan ya fadi a zaben. A yanzu haka yan takaran gwamnan jihar akalla 33 sun yi taron dangi kan mataimakin gwamnan jihar domin tunbukeshi daga mulki a zaben da za'a gudanar a watan Yuli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel