Shugaba Buhari ya yi bukin ranar demokradiyarsa ta karshe - Uche Secondus

Shugaba Buhari ya yi bukin ranar demokradiyarsa ta karshe - Uche Secondus

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya yi bukin zagayowar ranar demokradiyarsa ta karshe kenan a matsayinsa na shugaban kasa.

A cewarsa, Najeriya da demokradiyar mu ba za ta daure ba idan har shugaba Buhari ya zarce.

A sakon ranar demokradiyarsa da ya aike ta hannun mai magana da yawunsa Ike Abonyi, Secondus ya ce "Yan Najeriya sun matsu da jiran damar da za su kawar da jam'iyyar APC da shugaba Buhari."

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci taliyar karshe - Uche Secondus

Shugaba Muhammadu Buhari ya ci taliyar karshe - Uche Secondus

Ya ce a ranar irin wannan, 'yan Najeriya ya kamata su rika murnar samun walwala ne da shugabancin na nagari a maimakon "kokawa da matsanancin halin rayuwa da suke ciki".

KU KARANTA: Wasu jami'o'i uku a Najeriya za su fara digiri a fanin nazarin magungunan gargajiya

Sanarwar ta cigada da cewa: "idan dai muna son demokradiyya ta daure a wannan kasar, dole ne muyi waje da APC kuma a yanzu yan Najeriya a shirye suke saboda sunyi imani cewa demokradiya ce mafi kyawun tsarin shugabanci.

Idan akayi la'akari da cewa shugaban kasar bai tabuka komai ba cikin watanni 36 da suka gabata da kuma yunkurin yan Najeriya na daura kasar a kan turba mai kyau, wannan ce ranar demokradiya ne karshe da shugaban kasan zai yi, inji Secondus.

Ya kuma cigaba da cewa ranar demokradiya mai zuwa wato 29 ga watan Mayun 2019, wanda yan Najeriya ke sa ran gani za ta kasance ranar mika mulki ne daga gwamnatin da bata da alkibla zuwa demokradiya ta ainihi wanda PDP za ta jagoranta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel