An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

Rahotanni sun kawo cewa an karrama babban jigon Arewa kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Balarabe Musa ta hanyar sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunansa.

Da yake jawabi a yayin bikin bude Asibitin wanda ya gudana a Unguwar Bagado Kamazoo yankin Karamar Hukumar Chikum ta Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar la'akari da halin kunci da kuma takura da Jama'ar yankin ke ciki dangane da batun kiwon lafiyar su, ya sanya shi zabura wajen gina musu Asibiti na zamani domin amfanin su da 'ya'yansu harma da jikoki wadanda za su zo anan gaba.

Sanatan mai wakiltar shiyyar Kaduna ta tsakiyan ya kuma kara da cewar, ya sanya wa Asibitin sunan Dattijo tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa, bisa ga irin kokarin da Dattijon ya ke da shi na kishi gami da taimakon talakawa inda ya bayyana shi a matsayin abin koyi ga Shugabanni na kwarai.

An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

Da yake nuna farin cikinsa, Balarabe Musa ya ce ya ji dadigami da farin ciki akan kwazo da kokarin Sanata Shehu Sani, wanda ya bayyana shi a matsayin wakili nagari kuma Shugaba wanda ya damu da damuwar Jama'ar shi.

An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

An sanya wa katafaren Asibitin da Sanata Shehu Sani ya gina sunan Balarabe Musa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Sanata Shehu Sani ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamnan jihar Kaduna a zaben 2019, inda yace mulkin El-Rufai ya kusa zuwa karshe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a shafukanmu:

https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel