Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

- Tusa ta karewa bodari, bayan shiga hannun 'Yan sanda da yaji matsa ya fara bayani

- Korarren Dan sandan da ya shiga sana'ar Fashi da Makami ya ce daukar fansa yayi

- A cewarsa domin ya koya musu darasi

Daya daga cikin wanda suka yi fashin Banki a garin Offa dake jihar Kwara, wato Michael Adikwu wanda tsohon Jami'in 'Dan sanda ne ya bayyana cewa shi ne mutumin daya shirya komai dangane da fashin da aka yi a ranar 5 ga watan Afrilun da ya gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane har 30.

Adikwu ya ce ya aikata hakan ne bisa rashin adalcin da aka masa na korarsa daga bisa rashin ka'ida.

Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

Adikwu ya ce ya samo ragowar mutanen da suka goya masa baya domin aiwatar da fashin, inda suka kai hari a caji ofis din Offa domin jan-kunne ga jami'an 'yan sandan Najeriya.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa fitaccen Dan sandannan ne wato mataimakin Kwamishinan 'Yan sanda Abba Kyari ne ya jagoranci kamo Adikwu da kuma shugaban rukunin yaki da fashi da Makami na jihar ta Kwara (SARS), a wani sumame da suka kai. Kuma bincike ya nuna cewa Adikwu ya kashe jami'an 'yan sanda har mutum 6 a yayin da suka kai wancan farmaki.

Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

Yadda na shirya komai dangane da fashin da muka yi a garin offa - Tsohon jami'in Dan sanda

KU KARANTA: Ranar demokradiyya: Gwamna Badaru ya umurci mutanen jihar Jigawa da su zauna cikin gida

Daga cikin wanda aka yi nasarar cafkewa akwai wanda ake kira da Kunle Ogunleye wanda akewa lakabi da "Arrow", shi kansa ya bayyanawa cewa ya kashe mutane har guda 2. Sai kuma Abel wanda shi ma yana daga cikin wanda aka yi nasarar damkewa, shi ma ya ce ya kashe mutane har guda 5.

"Na harbi mutane da dama amma ba zan iya tabbatarwa da guda nawa ne suka mutu ba, sai dai a lokacin nasan guda 5 sun mutum a take amma baya ga wannan ban sani ba ko daga ba wanda suka ji rauni wani shi ma ya mutu".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel