Ranar Jimami: ‘Yan Najeriya sun roki shugaba Buhari da ya magance kisan da akeyi a fadin kasar

Ranar Jimami: ‘Yan Najeriya sun roki shugaba Buhari da ya magance kisan da akeyi a fadin kasar

- Daya daga cikin shataletalen da akafi amfani dashi a jihar Legas, shataletalen Allen, wanda ke kilo 2.9 daga sakatariya ta cushe sakamakon mutane 300 maza da mata da suka taru domin jimamim mutunen da aka kashe a fadin kasar

- Mutanen sanye da bakaken kaya sunyi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya kawo karshen wannan kashe kashe da ake tayi a fadin kasar

- Mutanen sun bukaci zaman lafiya a ko ina na fadin kasar, Dr. Abiola Akiyode-Afolabi, mai magana da yawun kungiyar mata masu bincike da neman ‘yanci, yace a yau suna nuna rashin jin dadinsu game da kisan da akeyi a fadin kasar nan

Daya daga cikin shataletalen da akafi amfani dashi a jihar Legas, shataletalen Allen, wanda ke kilo 2.9 daga sakatariya ta cushe sakamakon mutane 300 maza da mata da suka taru domin jimamim mutunen da aka kashe a fadin kasar.

Mutanen sanye da bakaken kaya sunyi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya kawo karshen wannan kashe kashe da ake tayi a fadin kasar, suna tafe suna wakokin jimami a cikin yarirrika kala-kala na fadin Najeriya.

Mutanen sun bukaci zaman lafiya a ko ina na fadin kasar, Dr. Abiola Akiyode-Afolabi, mai magana da yawun kungiyar mata masu bincike da neman ‘yanci, yace a yau suna nuna rashin jin dadinsu game da kisan da akeyi a fadin kasar nan.

Ranar Jimami: ‘Yan Najeriya sun roki shugaba Buhari da ya magance kisan da akeyi a fadin kasar

Ranar Jimami: ‘Yan Najeriya sun roki shugaba Buhari da ya magance kisan da akeyi a fadin kasar

“A yau muna tinawa jimamin wadanda ‘yan kungiyar Boko Haram, da ‘yan ta’addan Filani da kuma masu satar mutane suka kashe, da kuma mata wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rashin ingantaccen dakin haihuwa a asibitoci.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan Najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar yanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel