Tinubu ya fara zawarcin wasu fitattun ‘yan Najeriya biyu domin karawa jam’iyyar APC karfi

Tinubu ya fara zawarcin wasu fitattun ‘yan Najeriya biyu domin karawa jam’iyyar APC karfi

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya yi kira ga babban lauya Mista Femi Falana da fitaccen dan jarida, Mista Kunle Ajibade das u shigo jam’iyyar APC domin ciyar da Najeriya gaba.

A wani sakon murnar taya su murnar ranar zagayowar haihuwar su, Tinubu ya bayyana Falana da Ajibade a matsayin mutane da suka yi fice a bangaren aiyukan su sannan kuma suka bayar da gudunmawa wajen cigaban Najeriya.

An raba sakon na Tinubu ga fitattun mutanen ga ‘yan jaridar a yau, Litinin, a Legas ta hannun mai kula da ofishin yada labarai na Tinubu, Mista Tunde Rahman.

Tinubu ya fara zawarcin wasu fitattun ‘yan Najeriya biyu domin karawa jam’iyyar APC karfi

Bola Tinubu

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewar an haifi Falana ranar 20 ga watan Mayu, 1958 yayin da aka haifi Ajibade ranar 28 ga watan Mayu, 1958.

Tinubu ya kara da cewa, Falana da Ajibade sun bayar da gagarumar gudunmawa domin ganin an kori mulkin soja tare da kafa dimokradiyya a Najeriya.

DUBA WANNAN: APC ta lashe zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa

Kazalika ya bayyana godiyar sag a mutanen biyu bisa sadaukarwar su domin ganin an samu adalci da daidaito a Najeriya. Sannan ya kara da cewa, ya san hakan ne ta dalilin mu’amala da ta hada shi da abokanan junan biyu a gwagwarmayar sat a siyasa.

A karshe Tinubu ya bayyana cewar zai so ganin sun hada karfi da mutanen biyu domin yin tafiyar siyasa tare a cikin jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel