Ranar demokradiyya: Gwamna Badaru ya umurci mutanen jihar Jigawa da su zauna cikin gida

Ranar demokradiyya: Gwamna Badaru ya umurci mutanen jihar Jigawa da su zauna cikin gida

- Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, a ranar Talata, ya bukaci mutanen jiharsa dasu kasance a cikin gidanjensu a wwunin yau suna aduu’o’I domin cigaban jihar da kuma kasar baki daya

- Badaru, wanda yayi kiran lokacin da yake jawabi a taron manema labarai na ranar dimokuradiyya, yace kasar da shuwagabannin kasar suna bukatar addu’o’I domin sanin yadda zasu magance kalubalen da suke fuskanta

- Gwamna yace gwamnatinsa zata cigaba da kawo abubuwan cigaba na siyasa ga mutanen jihar ta jigawa

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru, a ranar Talata, ya bukaci mutanen jiharsa dasu kasance a cikin gidanjensu a wwunin yau suna aduu’o’I domin cigaban jihar da kuma kasar baki daya.

Badaru, wanda yayi kiran lokacin da yake jawabi a taron manema labarai na ranar dimokuradiyya, yace kasar da shuwagabannin kasar suna bukatar addu’o’i domin sanin yadda zasu magance kalubalen da suke fuskanta.

Gwamna yace gwamnatinsa zata cigaba da kawo abubuwan cigaba na siyasa ga mutanen jihar ta jigawa.

Ranar demokradiyya: Gwamna Badaru ya umurci mutanen jihar Jigawa da su zauna cikin gida

Ranar demokradiyya: Gwamna Badaru ya umurci mutanen jihar Jigawa da su zauna cikin gida

Badaru yace sati biyu da suka gabata, ya karbi bakuncin shugaba Muhammadu Buhari a jihar, wanda ya taimaka masa ya hada bayanai na cigaban gwamnatinsa a fannonin gwamnatin tasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

A baya Legit.ng ta rahoto cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan Najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar yanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel