Bangarori 4 da gwamnatin Buhari ta samu nasara da kuma bangorori 3 da ta gaza – Shehu Sani ya lissafa

Bangarori 4 da gwamnatin Buhari ta samu nasara da kuma bangorori 3 da ta gaza – Shehu Sani ya lissafa

Yayinda ake murnan zagayowar ranan demokradiyya a jihohin Najeriya 36 a yau, sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya yiwa wannan gwamnatin hisabi kan ayyukanta na shekaru 3 da suka gabata.

Sanatan da jam’iyyar APC shiyar jihar Kaduna ta dakatar ya bayyana wuraren da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta dan tabuka wani abu da kuma inda ta fadi warwas.

Daga cikin bangarorin da yace gwamnatin Buhari ta yi kokari shine wajen yaki da cin hanci da rashawa, dogaro da kai, karfafa tattalin arziki da kuma karashe ayyukan da gwamnatin baya ta bari.

Wuraren da kuma Buhari ya gaza a cewarsa sune kare mutuncin hakkin bil adama, kare rayukan al’amma da kuma kare mutuncin bangarorin gwamnati. Wannan na nuna cewa gwamnatin Buhari na mulki irin na kama karya.

KU KARANTA: Mahaddacin Alkur'ani ya rigamu gidan gaskiya

Ga jawabinsa: “Kasar nan karkashin wannan gwamnati ta samu nasara a bangarori na yaki da rashawa, dogaro da kai, tattalin arziki da karashe ayyuka. Kana ta gaza wajen kare hakkin bil adama, kare rayukan mutane da kuma kare mutuncin bangarorin mulki."

Wannan jawabi na zuwa ne bayan Sanatan ya alanta niyyar takaran kujeran gwamnan jihar Kaduna a jiya Litinin, 29 ga watan Mayu, 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel