Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari

Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari

Da sanadin shafi jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kalubale guda dake ci wa gwamnatin sa tuwo a kwarya a halin yanzu.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, sanadin asarar rayuka da dukiya da 'yan ta'adda na Boko Haram, masu garkuwa da mutane da kuma rikicin makiyaya da manoma a fadin a kasar nan shi ne babban kalubale da ya zamewa gwamnatin tarayya katutu a halin yanzu.

Jaridar ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan a yayin gabatar da jawaban sa na tunawa da ranar Demokuradiyyar Najeriya na shekarar 2018.

Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari

Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari

Yake cewa, gwamnatin sa tana iyaka bakin kokarin ta wajen tunkarar ta'addanci musamman na garkuwa da mutane, rikicin makiyaya da manoma da a halin yanzu ya salwantar da dumbin rayuka gami da asarar dukiya a cikin kasar nan.

KARANTA KUMA: Wani Mahaifi ya shiga hannu da laifin yiwa 'Ya'yan sa Mata 4 Fyade a garin Fatakwal

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya sha alwashi ga 'yan Najeriya cewa gwamnatin sa ba za ta gushe ba wajen ganin ta kawo karshen wannan barazana da ta zamto annoba cikin kasar nan.

Ya kara da cewa, tabbas gwamnatin sa za ta ci gaba da farauto dukkan masu hannu cikin wannan ta'asa tare da zartar da fushin dokin a kansu.

A yayin haka kuma, shugaba Buhari ya yabawa dakarun tsaro da sauran hukumomin tsaro dangane da jarumtar su akan kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.

Ya kuma yi jinjina da rundunonin hadin gwiwa na kasashen Nijar, Mali, Chad da kuma na Kamaru da suke bayar da gudunmuwar su wajen yakar ta'addanci a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel