Yajin aiki: Duk wanda ya bar aiki a asibiti ba zai samu albashi ba – Ministan lafiya

Yajin aiki: Duk wanda ya bar aiki a asibiti ba zai samu albashi ba – Ministan lafiya

- Ministan lafiya ya nemi Ma’aikaan lafiya su yi maza su koma bakin aiki

- Farfesa Isaac Adewole ya ba Malaman asibiti umarni su koma ofis maza

- Gwamnati tace duk fa wanda bai dawo aiki ba zai ji a asusun bankin sa

Mun samu labari dazu cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nemi Malaman asibitin Najeriya da su ke ta faman yajin aiki tun Watan Afrilu su yi maza su dawo bakin aiki. Dama Kotu ta nemi a janye yajin aikin tun kwanaki.

Yajin aiki: Duk wanda ya bar aiki a asibiti ba zai samu albashi ba – Ministan lafiya

Ministan lafiya Adewole ya bada umarni a janye yajin aiki

Ministan lafiya na Gwamnatin Tarayya karkashin Kungiyar JOHESU Farfesa Isaac Adewole ya ba Likitocin Najeriya umarni su koma wajen aikin su. Ministan ya bayyana wannan ne bayan da aka yi wani taro na musamman a makon nan.

Farfesa Isaac Adewole ya nemi manyan Darektocin asibitocin Kasar su nemi Ma’aikatan lafiya da ke fadin Kasar da ke yajin aiki su koma aiki. Darektan yada labarai na Ma’aiktar lafiya Baode Akinola ya bayyana wannan Ranar Litinin a Abuja.

KU KARANTA: Farfesa Sagay ya nemi a maka Obasanjo a Kotu

Isaac Adewole yace Gwamnati za ta dauki mataki da zarar Ma’aikatan sun cigaba da zama a gida. Ministan yace Gwamnati za ta dauka cewa Malaman asibitin sun bar aikin su ne ba tare da karbar hutu daga wajen aiki ba wanda babban laifi ne.

Gwamnati dai tace babu wanda ya ke da ikon rufe asibitoci a Kasar inda Ministan ya kara da cewa ba za a biya duk wadanda su ka shiga yajin aikin albashi ba. Ministan yace don haka su yi maza su koma bakin aiki kamar yadda Kotu ta bada umarni.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel