An bukaci Buhari ya hukunta 'yan majalisar da suka saci biliyan N481bn

An bukaci Buhari ya hukunta 'yan majalisar da suka saci biliyan N481bn

Wata babban kotun da ke zamanta a Legas ta umurci shugaba Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro da hukumomin yaki da rashawa su gaguta mika masa rahoton zargin karkatar da N481 biliyan daga kasafin kudin 2016 da aka ce wasu shugabanin majalisa sunyi.

Kotun har ila yau ta umurci shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Alkalin Alkalan kasa da Ministan Shari'a, Justice Abubakar Malami, SAN, tare da hukumomin yaki da rashawa da suka dace su gurfanar da 'yan majalisar da aka samu da hannu cikin badakalar a gaban kotu.

An bukaci Buhari ya hukunta 'yan majalisar da suka saci biliyan N481bn

An bukaci Buhari ya hukunta 'yan majalisar da suka saci biliyan N481bn

Alkalin kotun, Justice Muhammad Idris ya zartas da wannan hukuncin ne a jiya bayan wata kungiyar kwato hakkin talakawa da tabbatar da mulkin na gari (SERAP) ta shigar da wata kara mai lamba FHC/L/CS/1821/2017.

KU KARANTA: Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

Kotun kuma ta umurci shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa sakamakon binciken da hukumomin tsaron su kayi a kan zargin karkatar da kudadin daga kasafin kudin 2016.

A karar da aka shigar a kan shugaba Muhammadu Buhari da kuma Alkalin Alkalai da Ministan Shariah, Justice Idris, SERAP ta ce doka ta daura wa shugaban kasa nauyin tabbatar da cewa yan majalisar sunyi biyaya ga sashi na 22 na dokar kwato hakkin bil-adama da al'umma na Afirka.

Kotun ta ce SERAP a matsayinta na kungiya mai zaman kanta tana da ikon sanya idanu kan yadda ake kashe kudaden al'umma a kasar nan.

Mataimakin direktan SERAP, Timothy Adewale ya ce wannan hukuncin da kotun ta zartar ya tabbatar da zargin da akeyi na cewa akwai rashawa cikin yadda ake gudanar da kasafin kudin Najeriya kuma hukumomin da ya kamata su sanya idanu a harkar sun kawar da idanun su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel