Wani matashi yayiwa mahaifiyarsa duka har ta fita haiyyacinta bayan ya dawo daga gidan rawa cikin dare

Wani matashi yayiwa mahaifiyarsa duka har ta fita haiyyacinta bayan ya dawo daga gidan rawa cikin dare

- Wani matashi mai shekaru 32 ya shiga hannun jami’an tsaro na NSCDC a jihar Nasarawa, sakamakon duka da yayiwa mahaifiyarsa har ta fita daga hayyacinta

- Kwamandan Jami’an tsaron na NSCDC, Mohammed Gidado Fari, yace wanda ake zargin Obey Samuel, an kamashi ne sakamakon dukan da yayiwa mahaifiyarsa ba tare da wani uzuri ba

- Samuel yace bai duki mahaifiyar tasa ba kawai dai ya san da ya dawo gida yana cikin maye ya rufe mahaifiyar tasa ne a cikin daki kawai

Wani matashi mai shekaru 32 ya shiga hannun jami’an tsaro na NSCDC a jihar Nasarawa, sakamakon duka da yayiwa mahaifiyarsa har ta fita daga hayyacinta.

Kwamandan Jami’an tsaron na NSCDC, Mohammed Gidado Fari, yace wanda ake zargin Obey Samuel, an kamashi ne sakamakon dukan da yayiwa mahaifiyarsa ba tare da wani uzuri ba.

Samuel yace bai duki mahaifiyar tasa ba kawai dai ya san da ya dawo gida yana cikin maye ya rufe mahaifiyar tasa ne a cikin daki kawai.

Wani matashi yayiwa mahaifiyarsa duka har ta fita haiyyacinta bayan ya dawo daga gidan rawa cikin dare

Wani matashi yayiwa mahaifiyarsa duka har ta fita haiyyacinta bayan ya dawo daga gidan rawa cikin dare

Shugaban jami’an NSCDC ya tasa keyarsa tare da wasu mutane uku wadanda sukayi amfani da damar rikicin da akayi kwanannan tsakanin manoma da makiyaya a jihar suka sace kayayyakin mutane a gidajen da masu gidan suka gudu suka bari a karamar hukumar Keana.

KU KARANTA KUMA: Ranar demokaradiyya: Abubuwa da suka sanya jawabin shugaba Buhari na 2018 yayi shige da jawabinsa na 2016

Fari ya kara da cewa sun kama wani mutum da laifin damfarar bankin micro-finance kudi N85,000 da kuma wani mai laifin damfarar wani shima kudi N800,000. Yace dukkansu zasu turasu kotu domin karbar hukunci.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ‘Yan Sanda a jihar Binuwai sun kama wasu mutane uku masu safarar bindigogi wadanda suka hada da uba da dansa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel