Wani Magidanci ya yiwa 'Kanwar Matarsa 'Yar Shekara 14 Fyade a Jihar Legas

Wani Magidanci ya yiwa 'Kanwar Matarsa 'Yar Shekara 14 Fyade a Jihar Legas

A ranar Juma'ar da ta gabata ne wani magidanci mai shekaru 42 a duniya, Eze Onijekachi, ya gurfana a gaban kotun majistire dake zaman ta a unguwar Ebute Meta a jihar Legas da laifin murkushe kanwar matar sa da shekarunta ba su wuci 14 ba duniya.

Rahotanni da sanadin shafin jaridar The Punch sun bayyana cewa, Mista Eze ya aikata wannan aika-aika ne a gidan sa mai lamba 44 dake kan hanyar Joseph Babatunde a unguwar Ajanbadi ta jihar Legas.

Alkaliya mai shari'a, Misis A.O Adegite, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare Mista Eze a gidan kaso inda ta mika wannan lamari zuwa ga kotun laifuka na musamman dake birnin Ikeja.

Wani Magidanci ya yiwa 'Kanwar Matarsa 'Yar Shekara 14 Fyade a Jihar Legas

Wani Magidanci ya yiwa 'Kanwar Matarsa 'Yar Shekara 14 Fyade a Jihar Legas

A yayin haka kuma, Adegite ta shawarci Mista Eze akan neman belin sa a kotun mai sauraron karar laifuka na musamman kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

KARANTA KUMA: Jami'in Kwastam ya harbe Dattijo mai shekaru 70 daga shiga sulhunta sabani a jihar Oyo

Sufeto Onime Idowu, Jami'in dan sanda mai shigar da kara ya shaidawa kotun cewa, wannan laifi ya sabawa sashe na 137 cikin dokokin jihar ta Legas da aka tsara a shekarar 2015 da ta gabata.

Idowu ya kara da cewa, Mista Eze ya aikata wannan laifi ne da misalin karfe 2.00 na ranar 16 ga watan Mayu.

Legit.ng ta fahimci cewa, Mista Eze ya kai kwazabar sa ne kan kanwar matarsa da take taya su zaman daki da kuma kulawa da jaririn su a yayin da matarsa ta fita kwadago.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel