Sama da kasa ba za su hade ba idan Buhari ya maka Obasanjo a Kotu – Sagay

Sama da kasa ba za su hade ba idan Buhari ya maka Obasanjo a Kotu – Sagay

- Farfesa Itse Sagay yayi kira Gwamnatin nan ta Buhari ta binciki Obasanjo

- Mai ba Shugaban Kasar shawara kan cin hanci yace Obasanjo yayi ta’ada

- Sagay yace babu abin da zai faru idan aka maka Cif Obasanjo a gaban Kotu

Mai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin cin hanci da rashawa Farfesa Itse Sagay ya nemi a daure tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan badakalar wutar lantarki.

Sama da kasa ba za su hade ba idan Buhari ya maka Obasanjo a Kotu – Sagay

An ba Buhari shawarar ya kama Olusegun Obasanjo

Farfesa Itse Sagay ya nemi a kama tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo saboda kwangilolin bogin da yace an bada na wuta a lokacin yana mulki. Obasanjo ya kashe Dala Biliyan 16 wajen harkar wuta amma Najeriya ta cigaba da zama cikin duhu.

KU KARANTA: Manyan abubuwan da mu kayi a Gwamnatin nan - Buhari

Itse Sagay yace babu abin da zai faru idan aka binciki Obasanjo kan kudin da ya batar. Sai dai Farfesan yace bai ce a daure tsohon Shugaban Kasar ba sai dai a binciki ta’asar da yayi lokacin yana mulkin Kasar tsakanin 1999 har zuwa 2007.

Shi ma dai Kakakin Yakin neman zaben Shugaba Buhari watau Festus Keyamo ya goyi bayan wannan magana. Sai dai irin su tsohon ‘Dan Majalisar Kasar Dr. Junaid Mohammed da kuma Akin Oshuntokun sun yi tir da wannan kira da aka yi.

Sagay yace ba a kan Obasanjo aka fara binciken wani tsohon Shugaban Kasar ba. Farfesan yace babu dokar da ta hana a taba irin su Obasanjo. Mai ba Shugaban Kasar shawara yace ko zanga-zanga ba za ayi ba idan aka maka Obasanjo a Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel