Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

- ‘Yan Sanda a jihar Binuwai sun kama wasu mutane uku masu safarar bindigogi wadanda suka hada da uba da dansa

- Mutanen sune Thomas Ode alias Tommy, Kinsley Abi da mahaifinsa, Odah Abi, sune wadanda aka kama a garin Oju dake karamar hukumar Oju

- Labari yazo cewa an kama mutane dauke da kayayyakin da suka hada da bindigogi kala-kala tare da harsasai na samfurin bindigogi kala-kala

‘Yan Sanda a jihar Binuwai sun kama wasu mutane uku masu safarar bindigogi wadanda suka hada da uba da dansa.

Mutanen sune Thomas Ode alias Tommy, Kinsley Abi da mahaifinsa, Odah Abi, sune wadanda aka kama a garin Oju dake karamar hukumar Oju.

Legit.ng ta tattaro cewa an kama mutanen dauke da kayayyakin da suka hada da bindigogi kala-kala tare da harsasai na samfurin bindigogi kala-kala, sannan kuma an samesu dauke da wasu robobi guda biyu cike da tabar wiwi da kuma kwayar Tramadol kati biyar.

Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

Yanzu Yanzu: ‘Yan Sanda sun kama ‘yan ta’adda masu kera makamai da kuma fyade a jihar Binuwai

Kwamishinan ‘Yan Sanda, Fatai Owoseni, yace an kama wadanda ake zargin ne lokacin da ake gudanar da bincike akan garkuwa da mutane da kuma yiwa mata fyade.

KU KARANTA KUMA: Ranar demokaradiyya: Abubuwa da suka sanya jawabin shugaba Buhari na 2018 yayi shige da jawabinsa na 2016

Owoseni, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun kama wata yarinyar mai shekaru 15 sunyi mata fyade a kauyen, a ranar 21 ga watan Mayu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel