Ba sa ban ba: An ga Sanata Kwankwaso ba tare da jar hular sa ba a wajen taro

Ba sa ban ba: An ga Sanata Kwankwaso ba tare da jar hular sa ba a wajen taro

- Kwanakin baya ne aka karrama tsohon Gwamnan Kano a Garin Legas

- Mabiya ‘Darikar Katolika ne su ka ba Sanata Kwankwaso lambar yabo

- A wajen dai an ga tsohon Gwamnan babu jar hular sa da ya saba sa wa

Mun samu labari cewa manyan Kiristocin Duniya sun karrama tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Jihar yanzu a Majalisar Dattawa watau Rabi’u Musa Kwankwaso wajen wani taro da aka yi.

Ba sa ban ba: An ga Sanata Kwankwaso ba tare da jar hular sa ba a wajen taro

Kwankwaso babu jar hula lokacin da Limaman Kirista su ka ba shi kyauta

A makon da ya gabata ne a wajen wani taron Limaman Katolika na Duniya da aka yi a Garin Legas aka karrama tsohon Gwamnan na Kano kuma Jagoran tafiyar Kwankwasiyya a Kasar. A wajen taron an ga Sanatan babu hula a kan sa.

KU KARANTA: Barayin Kasar nan sun shiga uku sun lalace - Buhari

Bishof Idahosa da wasu manyan Malaman Addinin na Kirista su ka ba Sanatan Kano ta tsakiya lambar yabo na zama jajirtaccen shugaba a kasar. A ko yaushe dai an saba ganin Sanatan Kasar sanye da fararen kaya da kuma jar hula.

Wannan ne dai kusan karo na farko da aka ga tsohon Gwamnan na Kano babu jar hula wanda ta zama alamar ‘Darikar Kwankwasiyya. Kwanakin baya dai lokacin zaben Kananan Hukukomin Kano an ga Gwamna Ganduje babu hular.

Bayan Sanatan ya dawo daga Legas ne dai ya gana da Magoya bayan Kwankwasiyya daga Jihar Ebonyi domin jin yadda za a cigaba da tafiyar. Sanatan ya bayyana wannan ne a shafin sa na Tuwita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel