Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

- Bayan kammala tattaunawa da Mataimakin shugaban kasa Farfesa a fadar shugaban kasa dake Villa a Abuja jiya Litinin Mambobin sabuwar nPDP sun shaida cewa da sauran rina a kaba kan batun cigaba da zama a cikin Jam’iyyar ta APC

Mai magana da yawun 'ya'yan kungiyar Kawu Baraje ya bayyanawa manema labarai cewa wannan shi ne mafari yanzu nan gaba suna so su gana da shugaban kasa da kansa domin tattauna kan wasu muhimman batutuwa.

Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

A kwanakin baya ne 'yan sabuwar nPDP suka aikewa da uwar jam'iyyar APC ta kasa da takarda inda suka nuna rashin jin dadinsu game da yadda ake nuna halin ko in kula da kuma ware su daga cikin tafiyar gwamnatin ta APC duk da irin gagarumar gudunmawa da suka bayar wajen samun nasarar lashe zaben da jam'iyyar ta yi a kasa baki daya a 2015.

KU KARANTA: Kashe-Kashe na ci wa Gwamnatin Tarayya Tuwo a 'Kwarya - Buhari Author: Ishaq Ismail

Baraje ya bayyanawa manema labarai cewa "Mun aikewa da uwar jam'iyya ta kasa takarda kuma a cikin takardar mun hada shugaban kasa da kuma mataimakinsa. Uwar jam'iyya ta gayyace kuma mun amsa kira, yanzu kuma mun samu nasarar ganawa da mataimakin shugaban kasa, nan gaba kuma abin harin mu shi ne mu gana da shugaban kasa da kansa. Alhamdulilah da irin yadda Osinbanjo ya karbe mu sannan zamu zuba ido domin ganin an cika mana alkawarin da akai mana."

Baraje ya cigaba da bayani da "A halin yanzu dai an saka mu a cikin wasu kwamiti domin tattaunawa tare da nemo bakin zaren matsalar da kuma kawo karshenta, sai dai muna fatan ganawa da shugaba Buhari domin jin ta bakinsa."

Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

Bayan ganawa da Osinbajo, ‘yan nPDP Sun ce da saura dai, amma ba tabbacin zamansu a APC

Cikin wadanda suka samu damar halartar wannan zama da aka yi da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo sun hada da Shugaban Majalisar dattijai Bukola Saraki, Shugaban Majalisar wakilai Yakubu Dogara, Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan Jihari Kwara Abdulfatai Ahmed, da kuma Sanatan Kano ta tsakiya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel