Majalisar dattawa data wakilai suna kalubalantar Jega akan zarge-zargensa akan su

Majalisar dattawa data wakilai suna kalubalantar Jega akan zarge-zargensa akan su

Majalisar dattawa ta soki ikirarin da tsohon shugaban hukumar zabe na kasa yake yi mata Farfesa Attahiru Jega, na cewa masu cin hanci da rashawa sune suka mamaye majalisar

Majalisar dattawa data wakilai suna kalubalantar Jega akan battancin da yayi akan su

Majalisar dattawa data wakilai suna kalubalantar Jega akan battancin da yayi akan su

Majalisar dattawa ta soki ikirarin da tsohon shugaban hukumar zabe na kasa yake yi mata Farfesa Attahiru Jega, na cewa masu cin hanci da rashawa sune suka mamaye majalisar. Majalisar tace matsayin Jega bai kai ya dinga irin wadannan maganganun ba. Majalisar wakilai sun bukaci ya bayyana sunayen wadanda suke da hannu a cikin maganar da yayi.

DUBA WANNAN: Buhari zai ci koda kuwa babu nPDP - Sanata Abu Ibrahim

Mai magana da yawun majalisar dattawa, Aliyu Sabi Abdullahi, a jiya yace, matsayin Jega bai kai nan ba. Amma yace tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta yana da ra'ayin shi.

A wasance yace "Jega zai ma iya canza mana sunayen mu zuwa wanda yayi ra'ayi. Jega yana da ra'ayin shi. Duk abinda zai ce ma, bazai canza gaskiyar zance ba. Bazan maida martanin hakan ba. In yaso ma, ya maida sunayen mu ga duk wanda yayi niyya. Wannan shine abin sha'awa ga Dimokuradiyya. Mutane zasu iya fadin duk abinda suke so. Daidai ne hakan. Bazan maida martani game da abinda yace ba."

Amma majalisar wakilai sun kalubalanci Jega da yayi bayani akan zargin da yake yi ta hanyar bayyana masu cin hanci da rashawar a cikin su.

Kamar yanda mai magana da yawun majalisar wakilai, Abdulrazak Namdas, ya fada a wata tataunawar waya da yayi da manema labarai: "Mu dai mun san wannan zargi ne kawai yake yi. Zamu tabbatar muku da zargin ne idan Jega ya lissafo sunayen mutanen da yake nufi. Idan ya fada mana mutanen da suke karbar cin hanci, wannan abu daban ne. Wannan maganar da yayi, rufaffiya ce, bai kamata mu maida martani ba, mu dai munsan zargi ne kawai, har sai ya ambaci sunayen mutane sannan zamu maida masa martani."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel