Dalilin da yasa akwai bukatar ‘yan Najeriya su sake zabar Buhari a 2019 - Abubakar Bello

Dalilin da yasa akwai bukatar ‘yan Najeriya su sake zabar Buhari a 2019 - Abubakar Bello

- Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, a ranar Litinin, ya bayyana dalilai da dama wadanda suka nuna cewa ya kamata ‘yan Najeriya su sake jefawa Buhari kuri’a a zaben 2019

- Bello, ya bayyana cewa sake tsayawar Muhammadu Buhari takarar shugaban kasa a 2019, shine domin shimfida kwakwaran tubalin ginin cigaban damokradiyyar Najeriya

- Bello ya kara da cewa Buhari ne kadai jajirtaccen da ya tsaya kan kafafuwansa domin ganin cewa zaman lafiyan da aka wahala wurin ginawa ya dore a kasar nan

Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, a ranar Litinin, ya bayyana dalilai da dama wadanda suka nuna cewa ya kamata ‘yan Najeriya su sake jefawa Buhari kuri’a a zaben 2019.

Bello, ya bayyana cewa sake tsayawar Muhammadu Buhari takarar shugaban kasa a 2019, shine domin shimfida kwakwaran tubalin ginin cigaban damokradiyyar Najeriya.

Bello ya kara da cewa Buhari ne kadai jajirtaccen wanda ya tsaya kan kafafuwansa domin ganin cewa zaman lafiyan da aka wahala wurin ginawa ya dore a kasar nan, banda yaki da ‘yan ta’adda, da barayin shanu, da kuma masu garkuwa da mutane da yakeyi a fadin kasar.

Dalilin da yasa akwai bukatar ‘yan Najeriya su sake zabar Buhari a 2019 - Abubakar Bello

Dalilin da yasa akwai bukatar ‘yan Najeriya su sake zabar Buhari a 2019 - Abubakar Bello

Saboda haka yake kira ga mutanen Najeriya wadanda basu yi rajistar katin zabe ba, da suyi amfani da wannan damar ta rajistar katin zabe da ake tayi wurin ganin sun samu nasu katin zaben, saboda wannan ce kadai hanyar da zatasa wadanda ke neman komawa kujerarsu a jam’iyyar su koma.

KU KARANTA KUMA: Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

Abubakar Bello, ya kuma yi kira ga shuwagabannin jam’iyu da suyi kira ga zaman lafiya a cikin al’umma, domin hakan ne zaisa a samu gudanar da ingantaccen zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel