Ku magance matsalar rashin tsaro maimakon ku dorawa wasu laifi – Atiku ga gwamnatin tarayya

Ku magance matsalar rashin tsaro maimakon ku dorawa wasu laifi – Atiku ga gwamnatin tarayya

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga gwamnatin tarayya cewa ta magance matsalar rashin tsaro cikin kasar maimakon suyita zarge-zargen da baya karewa

- Atiku a jawabinsa na ranar damokradyyar Najeriya wanda aka fitar ta ofishinsa na sadarwa, a birnin tarayya, a ranar Litinin, yace matsalolin dake damun kasar suna bukatar ayi sabon tinanin wanda zai hada da kokarin da magabata sukayi wurin ganin sun raya siyasa

- Wazirin Adamawa, yace wadannan matsaloli da muke fuskanta cikin kasar sun isa hakanan saboda haka ya zama dole a maganacesu

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yayi kira ga gwamnatin tarayya cewa ta magance matsalar rashin tsaro cikin kasar maimakon suyita zarge-zargen da baya karewa.

Atiku a jawabinsa na ranar damokradiyyarr Najeriya wanda aka fitar ta ofishinsa na sadarwa, a birnin tarayya, a ranar Litinin, yace matsalolin dake damun kasar suna bukatar ayi sabon tinanin wanda zai hada da kokarin da magabata sukayi wurin ganin sun raya damokradiyya.

Wazirin Adamawa, yace wadannan matsaloli da muke fuskanta cikin kasar sun isa hakanan saboda haka ya zama dole a maganacesu.

Ku magance matsalar rashin tsaro maimakon ku dorawa wasu laifi – Atiku ga gwamnatin tarayya

Ku magance matsalar rashin tsaro maimakon ku dorawa wasu laifi – Atiku ga gwamnatin tarayya

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kara da cewa “Gwamnati ce kadai zata iya magance wadannan kashe-kashe marasa amfani da akeyi a fadin kasar nan, idan har ba so takeyi hadin kan da muke dashi a kasar ya tabarbare ba.”

KU KARANTA KUMA: Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

A halin da ake ciki, muin samu labarin cewa a jiya ne aka maka tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmud Aliyu Shinkafi da kuma tsohon Ministan Kasar watau Bashir Yuguda a gaban Kotu. Ana zargin su da karkatar da Naira Miliyan 450.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel