Tun bayan hawan Buhari: Duba adadin Mutanen da EFCC ta kama da kuma kudin da ta kwato

Tun bayan hawan Buhari: Duba adadin Mutanen da EFCC ta kama da kuma kudin da ta kwato

- An dade ana ta cecekuce kan kin bayyyan yawan kudin da Gwamnatin Buhari ta kwato daga hannun wadanda da EFCC ta kama, to amma a ranar Dimukuradiyya EFCC ta fasa kwai

- Inda hukumar ta bayyana yawan Mutanen da ta kama da kuma kudin da ta samu

- Kakakin hukumar Wilson Uwujaren ne dai ya ambata haka

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta bayyana cewa ya zuwa yanzu tun bayan hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2015 ta samu nasarar gurfanar da Mutane 603 bisa laifuka daban-daban da suke da alaka da cin hanci da rashawa.

Tun bayan hawan Buhari: Duba adadin yawan Mutanen da EFCC ta kama da kuma kudin da ta kwato

Tun bayan hawan Buhari: Duba adadin yawan Mutanen da EFCC ta kama da kuma kudin da ta kwato

EFCC ta kuma tabbatar da samun nasarar kwace zunzurutun kudin da ya kai N500bn a dai cikin shekaru uku na mulkin shugaba Buharin.

Hakan dai ya fito ne daga bakin kakakin hukumar Wilson Uwujaren a jiya Litinin inda ya bayyana cewa, sun samu nasarar gurfanar da Mutane 103 a shekarar 2015 da kuma 195 a shekarar 2016 da kuma 189 a shekarar 2017.

KU KARANTA: Duk mai rai mamaci ne: Yadda mamakon ruwan sama ya yi ajalin Alaramma, mahaddacin Qur'ani a garin Gombe

Sannan kuma a cikin watanni biyar na wannan shekara ta 2018 hukumar ta samu nasarar gurfanar da Mutane 116.

A cikin jawabin an bayyana cewa “Shugaba Muhammadu Buhari an dai zabe shi ne bisa alkawarinsa na yaki da mummunar al’adar nan ta Cin hanci da rashawa. Kuma hukumar ta EFCC ita ce jagaba a yakin da ake gwabzawa da masu yiwa arzikin kasa ta’annati.”

Daga cikin irin manyan nasarorin da hukumar dai ta samu har da hukunta manyan Mutanen da a da ake ganin kamar sun gagari kwandila ciki har da Manyan Sojoji da Manyan Alkalai har ma da wani babban Lauya mai lambar girma ta SAN.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel