Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida cewa babu mafaka da wadanda suka karkatar da dukiyar al'umma a yayin da suka rike wasu mukamai a kasar.

Shugaban kasan ya furta hakan ne a yayin da ya ke jawabinsa na ranar tunawa da zagoyowar ranar demokradiya wanda aka watsa misalin karfe 7 na safiyar yau.

Shugaban kasan ya bayyana cewa an sami nasarar kwato biliyoyin naira da yaki na rashawa da hukumomin EFCC da ICPC keyi da ma sauran wasu hukumomin yaki da rashawa da cin hanci.

Yaki da cin hanci da rashawar kuma ya yi sanadiyar kwato kadarori iri daban-daban wanda hakan ya kara darajar Najeriya a idanun kasashen duniya, inji shugaban kasan.

Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

Ranar Demokradiyya: Barayin dukiyar talakawa sun shiga uku - Shugaba Buhari

KU KARANTA: 2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje

Shugaba Buhari kuma ya ce gwamnatinsa da tana cigaba da aiki da kamfanonin da sukayi fice wajen gano kadarorin da aka boye a kasashe daban-daban na duniya tare da cin gajiyar yarjejeniyoyin da Najeriya tayi da wasu kasashen don yaki da rashawar.

"Nigeriya ta sanya a hannu a yarjejeniyar taimakawa juna ta hanyar shari'a don tabbatar da cewa dukkan wadanda suka sace dukiyoyin kasa basu da mafaka."

A cewar shugaban kasa, matakai da shirye-shirye da dama da gwamnatinsa keyi don magance cin hanci da rashawar sun fara haifar da sakamako masu amfani.

Wasu daga cikin matakan sun hada da asusun gwamnat guda daya (single treasury account) da shirin bayar da tukwuici ga wadanda suka tona asirin barayin gwamnati da gudanar da binciken kwakwaf a kan hukumomi da ma'aikatu da kwamitin shugaban kasa ta kirkiro da sauransu.

Shugaban kasan ya ce kasahen duniya sun fara mutunta Najeriya saboda matakan da suka ga gwamnatin na dauka wajen yaki da rashawa kana ya kuma lisafo wasu ayyuka da gwamnatinsa ke yi da wasu kudaden da ake ganowa da kashen wajen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel