2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje

2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya ce barazanar da tsaffin yan PDP da suka shigo APC (nPDP) keyi na ficewa daga jam'iyyar ta APC ba zai kawo wani cikas ba ga nasarar da shugaba Muhammadu Buhari zai samu a zabe mai zuwa.

Gwamnan ya kuma ce gunagunin da yan nPDP din keyi bata da tushe hasali ma dai kawai sharri suke nufin kulawa, ya kara da cewa basu da adadin magoya bayan da zai kawo wa shugaba Buhari wata cikas idan ma sun fice daga APC.

Ya kuma karyata ikirarin da wasu keyi na cewa ana nuna wariya ga wasu yan jam'iyyar inda ya ce wadanda ke koken ana nuna musu wariyar ma kalilan ne cikin wadanda suka baro jam'iyyar PDP suka dawo APC.

2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje

2019: Tsaffin 'yan PDP da suka dawo APC ba za su iya kawo wa Buhari cikas ba - Ganduje

KU KARANTA: Babban magana: Wata matashiya ta garzaya wata kotun Najeriya don neman izinin auren mace 'yar uwarta

Ganduje ya ce shi kansa dan nPDP ne wanda su kayi maja wajen kafa APC kuma ya tsame hannunsa daga cikin wadanda ke amfani da sunan nPDP wajen yadda jita-jitan cewa ana nuna musu wariyya a APC.

"Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki dan nPDP ne kuma yana da muhimman kwamitoci a karkashinsa wanda shine ya zabi shugabanin kwamitocin, wannan kawai ya nuna ba'a nuna wariyya ga mambobin nPDP." inji shi.

Ganduje kuma ya bayar da misalai da gwamnan jihar Adamawa da shi kansa inda ya ce dukkansu yan nPDP ne, kuma ya ce shi babu wanda ke nuna masa wariya.

"Ina kyautata zaton akwai wata makirci da ake shiryawa shugaba Buhari domin a yanzu yana fuskantar hare-hare daga wasu da suka karkatar da kudaden talakawa, ina tunanin abinda yasa wannan batun nuna wariyar ta taso kenan, za mu sa ido mu ga abinda zai faru." inji Ganduje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel