Transparency International ta nemi a soke kudin da ake warewa domin tsaro

Transparency International ta nemi a soke kudin da ake warewa domin tsaro

- Duk shekara Najeriya na ware makudan Dalolin kudi kan sha’anin tsaro

- Ana zargin Gwamnonin Kasar na karkatar da kudin ne a aljihun nan su

- An nemi Majalisa ta hana a daina ware wannan kudin a kasafin Najeriya

Yanzu haka dai an gano cewa shugabannin Najeriya na lashe makudan kudi duk shekara da sunan kudin tsaro sai dai har yanzu sha’anin tsaron akwai gyara musamman a Yankunan Kaduna, Benuwe, Filato, Taraba da dai sauran su.

Transparency International ta nemi a soke kudin da ake warewa domin tsaro

Ana zargin shugabanni da sace kudin tsaro a Najeriya

Hukumomin Transparency International ta Kasar waje da kuma CISLAC sun yi bincike inda su ka gano cewa Jihohi kusan 30 su ke kashe Dala Miliyan $580 kan harkar tsaro. Yanzu ma dai kudin da ake shirin kashewa bana zai dara na baya yawa.

Gwamnatin Buhari tayi kasafin akalla Dala Biliyan 1.2 ga sha’anin tsaro. Kusan dai ba a sa ido ga yadda ake kashe wannan kudi don haka masu ruwa-da-tsaki ke cin karen su babu babbaka. Yanzu dai an fara kira a tsaida ba Gwamnati wannan kudi.

KU KARANYA: Ba za mu yi maku irin na APC ba – Gwamnan PDP ya fadawa Matasa

Yanzu haka dai Gwamnatin Najeriya na neman zarar wasu makudan kudi daga asusun ta na rarar mai domin karasa yakar ‘Yan Boko Haram. Sai dai Jam’iyyar adawa ta PDP tace za ayi amfani da kudin ne domin murde zabe mai zuwa na 2019.

A ka’ida dai ana warewa Jihohi da Gwamnatin Tarayya kudin da ake cewa ‘Security Votes’ ne domin maganin tsaro. Sai dai ana zargin cewa masu mulki karkatar da kudin su ke yi don haka Transparency International ke kira a soke shi gaba daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel