2019: Idan mu ka samu mulki, za mu yi da Matasan Kasar nan – Gwamna Dankwambo

2019: Idan mu ka samu mulki, za mu yi da Matasan Kasar nan – Gwamna Dankwambo

Gwamnan Jam'iyyar PDP daya ne kacal ake da shi a kaf fadin Arewacin Najeriya kuma shi ne Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Jihar Gombe wanda yanzu hake yake harin kujerar Shugaban kasa.

2019: Idan mu ka samu mulki za mu yi da Matasan Kasar nan – Gwamna Dankwambo

Gwamna Dankwambo yace PDP ba za tayi irin na APC ba

Gwamnan na Gombe da ke neman shugaban Kasar nan yayi wa Matasan Najeriya alkawari cewa idan har Jam’iyyar adawa ta PDP ta samu mulkin Kasar nan a zaben 2019 to lallai za ta tafi da Matasa masu jini a jika cikin shugabanci.

Ibrahim Dankwambo yace PDP za ta zakulo Matasan da su ka san aiki domin a tafi da su a cikin Gwamnati. Gwamnan na Jam’iyyar adawa yace idan ta kai sai ayi yarjejeniya da Matasan Kasar nan na cewa za a dama su a siyasa.

KU KARANTA: Yadda Dankwambo ya gama Jami'a yana shekara 22

Gwamnan na Jihar Gombe Ibrahim ‘Dankwambo mai shekaru 56 a Duniya yana cikin masu bugun gangar a ba Matasa dama su shigo harkar siyasa a Najeriya. Kwanaki Gwamnan yace tun yana Matashi aka fara damawa da shi a kasar.

Kamar yadda mu ka samu labari dai Gwamnan yayi wannan kira ne a shafin sa na Tuwita a makon nan inda yace ba za su yaudari Matasan Najeriya kamar yadda aka yi masu a baya-bayan nan ba.

Jiya kun ji cewa Fadar Shugaban Kasa ta yarda cewa akwai babbar matsala a Najeriya sai dai tace za a kai ga ci. Mataimakin Shugaban kasa ya kuma ce Yara su ne manyan gobe a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel