Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

Sanata mai wakiltan jihar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar da tallafi ga kimanin mutune 3007.

Sanata ya baiwa kowannensu jarin Naira dubu talatin (30,000) a yankin mazabar sa.

Wadanda suka amfana daga wannan tallafi dai sun fito ne daga kananan hukumomin Kano ta tsakiya guda 15 na kwaryar tsakiyar Kano.

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya rabawa matasa 3000 jarin 30,000 a Kano

Haka kuma, kimanin mata 120 ne suma suka ci gajiyar tallafin jari na Naira dubu 20,000 na matar Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari.

KU KARANTA KUMA: Yadda Rahama Sadau ke yi idan zata ci tuwon Shinkafa da miyan kuka

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa Mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbajo ya gana da jiga-jigan sabuwar PDP a yau Litinin, 28 ga watan Mayu.

Shugaban majalisar dattawa ne ya jagoranci mambobin sabuwar PDP zuwa wajen ganawar wanda ya gudana a gidan mataimakin shugaban kasar wato Aguda wanda ke fadar shugaban kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel