Mayakan Boko Haram 132 sun saduda, sun mika wuya ga dakarun soji

Mayakan Boko Haram 132 sun saduda, sun mika wuya ga dakarun soji

Hukumar sojin Najeriya ta sanar da cewar mayakan kungiyar Boko Haram 132 ne suka saduda tare da mika wuya ga rundunar soji a cikin wasu ‘yan kwanakin nan.

Hukumar ta kara da cewar, tana saka ran Karin wasu mayakan na Boko haram zasu ajiye makaman su tare da mika wuya a cikin ‘yan makonni masu zuwa.

Da yake nuna wadan da suka tuban ga manema labarai, shugaban rundunar Ofireshon lafiya Dole, Manjo janar Rogers Nicholas, ya bayyana cewar mayakan Boko Haram 17 daga Kala Balge da Kumshe sun mika wuya tare da kari da cewar, adadin mayakan kungiyar da suka tuba a cikin ‘yan makonnin da suka wuce ya kai 132. Mayakan sun fito ne daga yankunan Bama Monguno, Kala Balge, Damboa da Kumshe.

Mayakan Boko Haram 132 sun saduda, sun mika wuya ga dakarun soji

Mayakan Boko Haram

Kwamandan ya bukaci ragowar mayakan kungiyar Boko Haram da har yanzu basu mika wuya ba, da su fito daga maboyar su tare da mika wuya.

DUBA WANNAN: An kulla yarjejeniya tsakanin Iran da Israel a kan rikicin kasar Syria

Nicholas ya jaddada cewar kofar hukumar soji a bude take ga duk mayakin kungiyar Boko Haram dake son mika wuya tare da yin watsi da batun cewar suna kashe duk mayakin day a mika wuya bisa radin kan sa.

Daya daga cikin mayakan da ya mika wuya, Hassan Dahiru, ya ce tun farko an tilasta masu shiga kungiyar Boko Haram ne amma yanzu sun gane cewar kungiyar ba tana yaki ba ne don addinin Musulunci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel