Za mu shawo karshen matsalolin Kasar nan Inji Mataimakin Shugaban Kasa

Za mu shawo karshen matsalolin Kasar nan Inji Mataimakin Shugaban Kasa

- Mataimakin Shugaban kasa yace Gwamnatin Buhari ta san darajar yara

- Farfesa Yemi Osinbajo yace yara dai su ne manyan gobe a kowace Kasar

- Yemi Osinbajo yayi wannan jawabi ne a cocin da ke cikin Fadar Aso Rock

Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Najeriya na iya magance duk matsalolin da ke gaban ta. Yemi Osinbajo ya bayyana wannan ne a cocin Fadar Shugaban Kasa a karshen makon jiya.

Za mu shawo karshen matsalolin Kasar nan Inji Mataimakin Shugaban Kasa

Mataimakin Shugaban Kasa Osinbajo yace Najeriya za ta kai ga ci

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyanawa mutanen Kasar nan cewa ya san akwai matsala a Najeriya amma hakan ba zai hana a kai ga ci ba. Mataimakin Shugaban Kasar yace Najeriya na da duk abin da ya dace na shawo kan kalubalen da ke damun kasar.

KU KARANTA: Mun yi bakin kokarin mu daga kafa Gwamnatin APC - Buhari

Yemi Osinbajo yace kowace Kasa ta Duniya tana fama da irin kalubalen da Najeriya ta ke fuskanta. Osinbajo yace wannan Gwamnati ta dage wajen inganta rayuwar marasa galihu ta hanyar ciyar da marasa hali sama da Miliyan 8 a kowace rana.

Wannan ne karo na farko da Gwamnatin Tarayya ta ke ba yaran Makaranta a Jihohi sama da 20. Mataimakin Shugaban Kasar yace yara su ne manyan gobe don haka Gwamnatin Shugaba Buhari ta maida hankali a kan su domin gaba tayi kyau.

Kwanaki Fadar Shugaban Kasar ta bayyana cewa an samu karuwar kayan da Najeriya ke fita da su kasashen ketare a Gwamnatin Buhari. Yanzu Najeriya ta rage dogaro da arzikin man fetur.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel