Sanatoci da yan majalisan wakilai shahrarrun yan neman cin hanci ne - Farfesa Attahiru Jega

Sanatoci da yan majalisan wakilai shahrarrun yan neman cin hanci ne - Farfesa Attahiru Jega

Tsohon shugaban hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya daura kaulasa kan yan majalisan dokokin tarayya da neman cin hanci duk lokacin da za su gudanar sa ayyukansu da shari'a ya tanada.

Tsohon shugaban hukumar iNEC yayi jawabi ne a wani muhadaran murnan zagayowar ranan Demokradiyya a farfajiyar International Conference Centre, ICC Abuja a yau Litinin.

Farfesa Jega ya ce ya yi magana da shugabannin hukumomi da dama wadanda suka ikirarin cewa mambobin majalisar dokokin tarayya sun tambayesu makudan kudi da sunan wani aikin dube-dube.

Sanatoci da yan majalisan wakilai shahrarrun yan neman cin hanci ne - Farfesa Attahiru Jega

Sanatoci da yan majalisan wakilai shahrarrun yan neman cin hanci ne - Farfesa Attahiru Jega

A taron wanda shugaba Muhammadu Buhari, shugaban majalisan dattawan, Bukola Saraki; kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, da sauran manyan jami'an gwamnati suka halarta, farfesan ilimin siyasan ya ce "Wasu shugabannin kwamitocin a majalisan dokokin sun shahara da neman cin hanci."

KU KARANTA: 'Yar kunar bakin wake ta kashe Mutane 3 a Borno

Wannan jawabi da Jega yayi ya tabbatar da rahoton da ya bayyana kwanan nan inda shugabannin hukumomin gwamnati suka kai kukan yadda mambobin majalisan dokokin tarayya ke neman cin hanci a wajensu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel