Kasar Amurka ta dawo da wani dan Najeriya gida saboda latsa karamar yarinya

Kasar Amurka ta dawo da wani dan Najeriya gida saboda latsa karamar yarinya

- Wani dan Najeriya, Emmanuel Olugbenga Omopariola; mai shekaru 61, ya rasa shaidar sa ta zama dan kasar Amurka tare da tisa keyar sa zuwa gida, Najeriya

- Omopariola ya fara mika kan sa ofishin hukuma inda aka cigaba da tsare shi tun ranar 18 ga watan Afrilu kafin daga bisani a tisa keyar say a zuwa Najeriya, ranar 23 ga watan Mayu

- Omopariola ya shiga kasar Amurka ne a matsayin dalibi a shekarar 1983 kafin daga bisani ya samu shaidar kasancewar dan kasar Amurka a shekarar 2004

Wani dan Najeriya, Emmanuel Olugbenga Omopariola; mai shekaru 61, ya rasa shaidar sa ta zama dan kasar Amurka tare da tisa keyar sa zuwa gida, Najeriya, bayan ya amsa laifin latsa wata yarinya mai shekaru 7 a duniya.

Ofishin fitar da bakin haure daga cikin kasar Amurka da hadin gwuiwar hukumar kula da shige da fice da ta kwastam ne suka dawo da Omopariola gida, Najeriya, ranar 24 ga watan Mayu, 2018.

Kasar Amurka ta dawo da wani dan Najeriya gida saboda latsa karamar yarinya

Emmanuel Omopariola

Omopariola ya fara mika kan sa ofishin hukuma a garin Dallar inda aka cigaba da tsare shi daga ranar 18 ga watan Afrilu kafin daga bisani a tisa keyar sa ya zuwa Najeriya, ranar 23 ga watan Mayu, inda ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Mohammed dake Ikeja, jihar Legas.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun hallaka Fasto a harin da suka kai Cocin Katolika da safiyar yau a Taraba

Omopariola ya shiga kasar Amurka ne a matsayin dalibi a ranar 25 ga watan Maris, 1983 kafin daga bisani ya samu shaidar kasancewar dan kasar Amurka a ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2004.

Dawo da shi Najeriya ya biyo bayan wata doka da sashen shari’a na kasar Amurka ya kirkiro a watan Nuwamba na shekarar 2017, da ya bukaci a mayar da duk wanda aka samu da laifin yin lalata da kananan yara zuwa kasar sa ta haihuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel