Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

- Tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, ta kalubalanci daya daga cikin mambobin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, akan ikirarin da yayi na cewa ministar da jami’anta sun saka nasu kasafin cikin kasafin kudin kasa na 2015

- Misis Okonjo-Iweala, lokacin da take kokarin bada bayani akan lamarin a shafinta na tuwita, a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ikirarin da dan majalisar yakeyi ba daidai bane

- Ministar ta bayar da misalin na cewa a shekarar 2015 shugabannin majalisar wakilai sun hada kai da hafsoshin gwamnati domin kara N17bn cikin kasafin kudi na shekarar 2015

Tsohuwar ministar kudi, Ngozi Okonjo-Iweala, ta kalubalanci daya daga cikin mambobin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, akan ikirarin da yayi na cewa ministar da jami’anta sun saka nasu kasafin cikin cikin kasafin kudin kasa na 2015.

Misis Okonjo-Iweala, lokacin da take kokarin bada bayani akan lamarin a shafinta na tuwita, a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ikirarin da dan majalisar ya keyi ba daidai bane.

Ministar ta bayar da misalin na cewa a shekarar 2015 shugabannin majalisar wakilai sun hada kai da hafsoshin gwamnati domin kara N17bn cikin kasafin kudi na shekarar 2015.

Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

Mista Gbajabiamila, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, wanda kuma a shekarar 2015 ya kasance shugaban marasa rinjaye a majalisar, yace bashida masaniyar cewa ‘yan majalisar sun karbi wani cin hanci.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa kawai an kara kudaden ayyukan majalisar ne a lokacin saboda haka babu yanda za’ayi a kirashi da cin hanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel