Dole zaben 2019 ya kasance mai inganci kamar na 2015 - Saraki

Dole zaben 2019 ya kasance mai inganci kamar na 2015 - Saraki

- Shugaban majalisar Dattijai Bukola Saraki, a ranar Litinin yayi gargadin cewa zaben 2019 mai zuwa kada ya kasa ingancin wanda aka gudanar 2015

- Saraki ya bayyana haka a sakon fatan alkhairi da ya gabatar a wurin taron bikin ranar damokradiyya ta shekarar 2018, wanda akayi a birnin tarayya

- Saraki ya gargadi ‘yan Najeriya akan daukar siyasar Najeriya a matsayin abun wasa ko kuma mara muhimmanci

Shugaban majalisar Dattijai Bukola Saraki, a ranar Litinin yayi gargadin cewa zaben 2019 mai zuwa kada ya kasa ingancin wanda aka gudanar 2015.

Saraki ya bayyana haka a sakon fatan alkhairi da ya gabatar a wurin taron bikin ranar damokradiyya ta shekarar 2018, wanda akayi a birnin tarayya.

Saraki ya gargadi ‘yan Najeriya akan daukar siyasar Najeriya a matsayin abun wasa ko kuma mara muhimmanci.

Dole zaben 2019 ya kasance mai inganci kamar na 2015 - Saraki

Dole zaben 2019 ya kasance mai inganci kamar na 2015 - Saraki

Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, a nashi jawabin ya bayyana siyasar Najeriya a matsayin mara karfi, saboda haka ya bukaci mutanen Najeriya da suyi iya kokarinsu don ganin cewa siyasa ta rayu a Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Jami’an tsaro sun kama wasu mata biyu da jarirai

Tsohon shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Farfesa Attahiru Jega, shine mai gabatar da jawabi a wurin taron, sannan shugaba Muhammadu Buhari zai jagoranci manyan jami’an gwamnati zuwa wurin taron.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel