Babu abinda suka fi razana ni game da zaben 2019 kamar abubuwa guda 2 – Inji Jega

Babu abinda suka fi razana ni game da zaben 2019 kamar abubuwa guda 2 – Inji Jega

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Attahiru jega ya bayyana cewa abubuwa guda biyu zuwa uku da ka iya zama tarnaki game da zaben 2019 suna tayar masa da hankali a duk lokacin da ya tuna su.

Jaridar Punch ta ruwaito Jega ya bayyana haka ne a yayin taron lakca da aka shirya don bikin ranar Dimukradiyya, da ya gudana a babban daki taro na kasa da kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Cinnen EFCC: Cikin jiga jigan yayan jam’iyyar PDP ya duri ruwa

“Ina tsoron barkewar rikici, da furta kalaman batanci zasu iya kawo ma zaben 2019 tarnaki, baya da haka, jan kafa da yan majalisa suke yi game da kammala aiki akan da sabbin dokokin zabe, da kuma rashin jituwa a cikin gidan jam’iyyu zasu zamo manyan mtsaloli ga zaben 2019.” Inji Jega.

Babu abinda suka fi razana ni game da zaben 2019 kamar abubuwa guda 2 – Inji Jega

Attahiru Jega

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bacin ranshi ga sakataren gwamnatinsa, Boss Mustapha sakamakon rashin gayyato Godsday Orubebe, mutumin nan da ya nemi ya tayar ma Jega hankali a lokacin da ake kirga kuri’un shugaban kasa na zaben 2019, zuwa taron don ya saurari maganganun da Jega zai yi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel