Duba kaga irin kudaden da gwamnatin tarayya ta samu cikin shekara daya dalilin wasu tsare-tsare data canja a kasar nan

Duba kaga irin kudaden da gwamnatin tarayya ta samu cikin shekara daya dalilin wasu tsare-tsare data canja a kasar nan

A ranar Lahadi dinnan ne, Ministar kudi Femi Adeosun, tace a tsakanin shekarar 2016 da 2017 gwamnatin tarayya ta tara naira biliyan 125 ta hanyar rage kudin alawus din tafiye - tafiye, alawus din zaman majalisa da sauransu

Gwamnatin tarayya ta samar da naira biliyan 125 a shekara daya dalilin wasu tsare-tsare data canja a kasar nan

Gwamnatin tarayya ta samar da naira biliyan 125 a shekara daya dalilin wasu tsare-tsare data canja a kasar nan

A ranar Lahadi dinnan ne, Ministar kudi Femi Adeosun, tace a tsakanin shekarar 2016 da 2017 gwamnatin tarayya ta tara naira biliyan 125 ta hanyar rage kudin alawus din tafiye - tafiye, alawus din zaman majalisa da sauransu.

Tace an samar da kudin ne ta bangaren rage wasu abubuwa wanda basu da muhimmanci a gwamnatance, wanda hukumar ta tsara domin rage kashe - kashen kudade babu gaira babu dalili.

DUBA WANNAN: Duk da matsalar tattalin arziki a Najeriya, munyi aiki fiye da yanda ake tunani - Gwamnatin Tarayya

A dokokin da hukumar ta saka ya hada da bada takardu ga ma'aikatu, bangarori da cibiyoyin gwamnati, sannan kuma ta shawarce su da suyi amfani da kashi biyar zuwa kashi hamsin wajen siyan tikitin jirgi.

Anyi haka ne don rage kudaden da ake kashewa na gwamnati.

Ministan tace sanadiyyar tsarin da gwamnatin ta kawo an samu naira biliyan 91 ta bangaren rage alawus din tafiye - tafiye tsakanin shekarar 2016 zuwa 2017, naira biliyan 34 kuma ta bangaren rage kudin sayen kayayyakin ofisoshin gwamnati.

Ministar tace "Gwamnatin ta rage kashe kudaden ne inda ta rage kudin takardun takardun da ake rabawa sakatarorin gwamnatin tarayya, shugabannin ma'aikatun gwamnatin tarayya da kuma albashin kasar, hadi da kudin kamasho."

"Gwamnatin ta samar da naira biliyan 34 na tafiye - tafiye a shekarar 2016 da kuma naira biliyan 57 a shekarar 2016. Sannan a bangaren kayayyakin ofis da abubuwan na'urori gwamnatin ta samar naira biliyan 24 a shekarar 2016 da kuma naira biliyan 10 a shekarar 2017."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel