Kotu ta jefa barayin mai 12 gidan yari

Kotu ta jefa barayin mai 12 gidan yari

- Bayan shekaru 3, an yankewa barayin mai 12 hukunci

- Sun aikata wannan laifi tun shekarar 2014 amma sai yanzu kotu ta kawo karshen karan

Babban kotun tarayya da ke zaune a Legas ta tura barayin mai 12 da suka saci litan man gas 600,000 ba bisa ga doka ba.

Alkalin mai sunan Jastis Mohammed Idros, ya tuhumcesu da almundahana, kamar yadda hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da su.

Barayin man sune Christopher Okorie, John Mbah, Tammy Bami, Osi Prince, Chukwuji Festus, da Kabiru Adeyemo.

Sauran sune Ayannubi Moses, Sopuruchukwu Chukwudi, Obinna Ebu, Abdullahi Oyelade, Charles Ubey da Achia Vincent.

Lauyan EFCC, Ekene Iheanacho ya bayyanawa kotu cewa wadannan barayi sun aikata laifin ne tsakanin watan Disamba 2014 da Satumba 2015.

Kotu ta jefa barayin mai 12 gidan yari

Kotu ta jefa barayin mai 12 gidan yari

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa EFCC ta tasa keyar babban sakataren gwamnatin jihar Ribas mai suna Mista Kenneth Kobani tare da wani dan siyasa a jihar mai suna Samuel Okpoko zuwa kotu bisa zargin laifuka 6.

KU KARANTA: Karanta yadda karuwai 'yan Najeriya ke rayuwa a Turai

Kamar dai yadda muka samu, cikin laifukan da ake tuhumar mutanen hadda kuma laifin karbar kudin haram da suka kai Naira miliyan 750 daga hannun tsohuwar ministar man fetur a lokacin gwamnatin da ta gabata ta Goodluck Jonathan Diezani Alison- Madueke.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel