Da dumin sa: ‘Yan bindiga sun kai hari wata cocin jihar Taraba, sun harbe Fasto

Da dumin sa: ‘Yan bindiga sun kai hari wata cocin jihar Taraba, sun harbe Fasto

Wasu ‘yan bindiga, da rahotanni suka bayyana cewar ana zargin makiyaya ne, sun kai wani hari wata Cocin Katolika dake Jalingo, jihar Taraba, da safiyar yau.

Jaridar Daily Trust a rawaito cewar wasu limaman Cocin da dalibai sun samu raunuka yayin da ‘yan bindigar suka kai harin.

Da dumin sa: ‘Yan bindiga sun kai hari wata cocin jihar Taraba, sun harbe Fasto

Limaman Cocin Katolika

Evaristus Bassey, darekta a wata kungiya dake karkashin kulawar Cocin Katolika, ya tabbatar wa da jaridar The Cable dake watsa labarai a yanar gizo, batun kai harin.

DUBA WANNAN: APC ta lashe zaben kananan hukumomin jihar Nasarawa

Rahotanni sun bayyana cewar an harbe wani limamin cocin yayin da wasu mutum biyu suka samu raunuka.

Zamu kawo maku Karin bayani dangane da wannan batu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel