An damke wasu tsageru 3 da suka lalata Na’urar da take bawa gidan shugaba Buhari wutar lantarki

An damke wasu tsageru 3 da suka lalata Na’urar da take bawa gidan shugaba Buhari wutar lantarki

- An yi ram da wasu Mutane 3 da safiyar jiya Lahadi bisa lalata na’aurar dake kai hasken wutar lantarki gidan shugaban kasan Muhammdu Buhari dake kan titin Sultan a jihar Kaduna

- Hukumar samar da wutar lantarki ta jihar ce ta bayyana hakan

Wani jawabi daga bakin shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar samar da wutar lantarki ta jihar Kaduna Abdulazeez Abdullahi ya ce tsageru ukun da aka kama sun lalata wayar da take kaiwa Transfomar wuta wanda hakan ya bawa mazauna yankin matsalar samun wutar latarkin.

An damke wasu tsageru 3 da suka lalata Na’urar da take bawa gidan shugaba Buhari wutar lantarki

An damke wasu tsageru 3 da suka lalata Na’urar da take bawa gidan shugaba Buhari wutar lantarki

KU KARANTA: Har yanzu Talakawa na tare da Buhari – Garba Shehu

Sannan ya kara da cewa wadanda aka Kaman din an kai su Ofishin ‘Yan sanda na Unguwan Rimi domin tattara su a gurfanar da su gaban alkali da zarar an kammala bincike.

daga nan ne Abdulazeez ya bukaci abokan huldarsu da su agaza musu wajen magance irin wannan muguwar ta’ada ta lalatawa ko sace kayayyakin samar da wutar lantarkin domin a cewarsa, shi ne babban taimakon da jama’ar gari zasu iya bayarwa wajen tabbatuwar samuwar wutar lantarki isasshiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel