Ma’aikatan kamfanin mai 28 sun makale, amma an ceto wasu 100 daga gobarar data tashi a kamfanin mai na Conoil

Ma’aikatan kamfanin mai 28 sun makale, amma an ceto wasu 100 daga gobarar data tashi a kamfanin mai na Conoil

- Bincike ya nuna cewa 28 cikin ma’aikatan kamfanin ConOil dake garin Koluama 1, a jihar Bayelsa, ne suke makale cikin kamfanin sakamakon gobarar data tashi a kamfanin a ranar Asabar

- Anyi nasarar ceto ma’aikatan kamfanin sama da 100 a jiya

- Gobarar ta tashi ne da misalign karfe 5 na safe a ranar Asabar, wadda yayi sanadiyar fashewar tankin man dake kamfanin sannan ta wuce zuwa gidajen ma’aikatan kamfanin dake cikin harabar kamfanin

Bincike ya nuna cewa 28 cikin ma’aikatan kamfanin ConOil dake garin Koluama 1, a jihar Bayelsa, ne suke makale cikin kamfanin sakamakon gobarar data tashi a kamfanin a ranar Asabar, kamar yadda majiyarmu ta ruwaito.

Anyi nasarar ceto ma’aikatan kamfanin sama da 100 a jiya, cikin wadanda gobarar ta ritsa dasu a cikin harabar kamfanin man na ConOil dake garin Koluama, a jihar Bayelsa.

Ma’aikatan kamfanin mai 28 sun makale, amma an ceto wasu 100 daga gobarar data tashi a kamfanin mai na Conoil

Ma’aikatan kamfanin mai 28 sun makale, amma an ceto wasu 100 daga gobarar data tashi a kamfanin mai na Conoil

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na safe a ranar Asabar, wadda yayi sanadiyar fashewar tankin man dake kamfanin sannan ta wuce zuwa gidajen ma’aikatan kamfanin dake cikin harabar kamfanin, kamar yadda rundunar jami’an tsaro na garin Niger Delta suka tabbatar.

KU KARANTA KUMA: Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

Ma’aikatan wadanda aka ceto an tafi dasu garin Patakwal a jihar Rivers. Inda wasu kuma har yanzu suke makale a gidajensu dake cikin harabar kamfanin, inda ma’aikatan kwana-kwana da jama’ar garin keta kokarin kashe gobarar domin ceto rayukan wadanda ke makale a ciki.

Mai magana da yawun hukumar kisan gobarar, Mal. Abdullahi Ibrahim, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya bayyana cewa duka ma’aikatan dake aiki a bakin rijiyar man anyi nasarar ceto su, sannan kuma har yanzu ba’a rasa rai ba ko daya sakamakon gobarar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel