Har yanzu Talakawa na tare da Buhari – Garba Shehu

Har yanzu Talakawa na tare da Buhari – Garba Shehu

- Da alama sukar da ake yiwa Gwamnatin tarayya baya mata dadi

- Domin ta bazama wanke bakin fentin da 'yan adawa suke kokarin shafa mata da cewa ta gaza

- Yanzu haka fadar shugaban kasa ta umarci duk Ministocinta da su yiwa Mutane bayanan nasarar da Gwamnatin APC ta samu tun bayan hawanta mulki

Ko yau aka kada gangar zabe Talakawa tabbas zasu zabi Buhari a 2019 domin sun yi amanna cewa yana yin iyakar kokarinsa. Wadannan kalamai na fitowa daga bakin babban mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai Garba Shehu.

Har yanzu Talakawa na tare da Buhari – Garba Shehu

Garba Shehu

Shugaba Buhari dai na cigaba da fuskantar suka daga manyan jiga-jigan jam’iyyar adawa musamman PDP. Sai dai kuma Shehu ya bayyana cewa a lokacin da jam’iyyar PDP ludayinta yake kan dawo babu wata doka da basu yiwa karan tsaye ba, a don haka yanzu sai su ja bakinsu suyi shiru kawai.

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku ya naɗa wani tsohon gwamna a matsayin shugaban yakin neman zabensa

Fadar shugaban kasa ta bayyana a jiya cewa Ministoci su shiga kafafen yada labarai domin su labarta irin namijin kokari da kuma nasarorin da Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samar tun bayan hawanta mulki kimanin shekaru uku, a wani fanni na shagulgulan ranar Dimukuradiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel