Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

- Jam'iyyar PDP ta ce babu wani amfani da bikin zagayowar dimokradiyya zai yi wa 'yan Najeriya

- A cewarta babu wani abu a cikin wannan mulki face tauye hakki

- Ta kuma zargi gwamnatin shugaba Buhari da takurawa dimokradiyya

Babbar jam'iyyar adawa wato jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP , ta ce babu wani amfani da bikin zagayowar dimokradiyya zai yi wa 'yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, PDP, ta ce, babu wani abu da 'yan Najeriya ke gani a cikin wannan mulki baya ga tauye hakkin dan adam.

Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

Bikin ranar dimokradiyya ba shi da amfani a Najeriya - PDP

KU KARANTA KUMA: Da ace Jonathan ya biya Jihar Osun kudin ta da ba haka ba - Aregbesola

Mataimaki na musamman a jam'iyar ta PDP a bangaren watsa labarai a yankin arewacin Najeriya, Shehu Yussuf Kura, ya bayyana cewa, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba ta dauki wani mataki na habbaka dimokradiyya ba a kasar, sai dai ma takura shi da yi masa zagon kasa.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon Shugaban Kasar Dr. Goodluck Jonathan ya karyata zargin sata inda yace sai da ya kammala ayyuka sama da 1000 a lokacin da yake rike da Kasar nan tsakanin 2010 zuwa 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel